Kebbi: Gobarar garin Zuru da Dabai, SEMA ta bayar da kayakin agajin gaggawa

Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kebbi SEMA ranar Asabar a garin Birnin kebbi ta bayar da kayakin taimako na gaggawa ga wadanda ibtila'in gobara ya rutsa da su a garin Zuru wanda ya shafi Kasuwar garin Dabai, Masallacin tsohuwar Kasuwar Zuru da wani gida da ya kone kurmus a unguwar road block dukka sakamakon gobara.

Shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru Alh. Muhammadu Kabir Abubakar ya karbi kayakin taimakon wanda nan take ya samar da mota da ta dauki kayakin zuwa Zuru, ya kuma bukaci a fara raba kayakin da zarar sun isa garin Zuru.

Alh. Muhammed Kabir Abubakar ya yi godiya ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu bisa kyakkyawar kulawa da ya yi tare da nuna damuwa a kan lamarin ta wakilinsa Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai wanda ya kai ziyarar jaje ga wadanda lamarin ya shafa.

Haka zalika shugaban karamar hukumar Zuru ya gode wa shugaban hukumar SEMA ta jihar Kebbi Alh. Sani Dododo bisa kokarinsa na ganin kayakin agaji sun isa hannun wadanda lamarin ya rutsa da su.

Kayakin da hukumar ta bayar sun hada da bondur 8 na kwanon rufi,buhu 28 na siminti domin kasuwar Dabai.Sai  Masallacin tsohuwar kasuwar Zuru bondur na kwanon rufi guda uku da buhun siminti guda biyar, sauran sun hada da bondur hudu na kwanon rufi,da kuma bondur biyu na kwanon rufi,buhu daya na dawa da masara buhu daya na gero, bargo uku, katifu hudu, Atamfa guda hudu, bondur uku na shedda da gidan sauro guda uku wanda aka ba gidan da yaro ya rasu a gobarar unguwar road block Zuru.

Daga Isyaku Garba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN