Abubakar Shikau ya arce sanye da hijabi - Sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nassarar kakkabe wani sansanin boko haram a dajin Sambisa a ci gaba da yaki da take yi da yan kungiyar ta Boko haram karkashin shirin rundunar ta Operation Lafia Dole da kuma Deep Punch 2 a sansanin yan boko haram.

Wata sanarwa da ta fito daga bakin kakakin rundunar soji na Najeriya Janar Kukasheka ya ce rundunar ta yi kaca-kaca da sansanin na boko haram kuma ta kama makamai da yawa yayin da 'yan kungiyar suka arce.

Kukasheka ya ce bayanai masu inganci da suka tattara sun nuna cewa shugaban kungiyar ta boko haram Abubakar Shikau ya yi shigar Mata sanye da hijabi ya tsere wa azabar matsi da soji ke yi wa yan koko haram.

Ya ce bayanan sun kara da cewa lokacin da aka gan Abubakar Shikau yana sanye da bakin hijabi kuma yakan canja ne daga bulu ko bakin hijabi kamar yadda wasu yan boko haram da aka kama suka shaida wa jami'an soji.

Kukasheka ya bukaci sauran yan boko haram da suke boye cewa su fito su mika makamansu domin a yi masu sassauci .

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN