• Labaran yau


  Ko ka san za a iya cutar da kai idan ka bayar da aron wayar ka na salula ?

  Sau da yawa wanda ke nesa da kai ba shi ne zai cuce ka a rayuwa ba, bincike ya tabbatar da cewa sau da yawa na kusa da kai ne ko dai shi ne zai cuce ka ko a hada baki da shi domin a cuce ka. A zamanin yau na kimiyyar sadarwa da ci gaba a harkar yanar gizo ya zama wajibi ka kula da abin da ke kai komo dangane da wayar salularka .

  Sakamakon ingancin zamani wajen aikatau da wayar salula, wani sabon salo da macuta suka gane shi ne sai su ce mutum ya ara masu waya za su kira wata lamba, idan ka basu wayar ka sai su danna *565*0# wanda zai bayyana lambobin ka na BVN wanda kai tsaye za a kwashe lambobin kuma daga lokacinnan mutumin zai karbe ragamar harkar Bankin ka kuma ya cutar da kai.

  Lambar BVN dai babban sirri ne da ke da muhimmanci kwarai. Domin shi ne garkuwa na sirrin huldar Bankin ka da kai kanka. Matukar wani ya san lambobin BVN da kake amfani da shi a hulda da Bankin ka, to lallai wani sharri zai iya biyowa baya, saboda haka sai a kiyaye.

  Hanya daya ita ce idan mutum ya bukaci wayar ka domin ya kira wata lamba, ka tabbata baka ba shi tazara  ba kuma ya yi duk abin da zai yi a gaban idon ka.

  Daga Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ko ka san za a iya cutar da kai idan ka bayar da aron wayar ka na salula ? Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama