Yadda aka gudanar da taron karshen shekara na APC a jihar Kebbi (Hotuna)

Isyaku Garba |

Jam'iyar APC ta jihar kebbi ta gudanar da babban taron ta na karshen shekara a filin wasa na Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi,wanda kuma 'yan Majalisar dokoki na jihar Kebbi suka yi amfani da shi suka gabatar da kuduri na tsayar da shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu domin su tsaya a takara a karkashin jam'iyar APC a 2019.

Sakataren Gwamnatin jihar Kebbi ya yi jawabi yadda aiki ya kasance karkashin wannan Gwamnati, ya kuma yi mamaki yadda har yanzu Matasa basu kammala cika gurbi na mutum 30.000 da ake bukata karkashin shirin N-power ba, ya ce mutum 8000 ne kawai suka yi rijista a karkashin shirin daga jihar Kebbi.

Kwamishinoni sun gabatar da tsarin yadda aka gudanar da ayyuka a Ma'aikatunsu, haka zalika babban Ma'ajin jihar Kebbi ya yi bayani dalla-dalla yadda Gwamnati ta kashe kudade a karkashin shuagabancin Sanata Atiku Abubakar Bagudu.

A nashi jawabi, Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu ya yi godiya ga Mataimakin Gwamna, Sanatoci,Ministan, kakakin Majalisar dokoki na jihar Kebbi tare da dukannin jama'a bisa dauriya da suka nuna  da kuma hakuri tare da ba Gwamnatinsa goyon baya.Haka zalika ya yi tsokaci akan lamura da suka shafi aikin gona da noman shinkafa, taimaka wa matasa, kiwon lafiya, tsaro da sauransu.

Taron ya sami halarcin masu ruwa da tsaki a jam'yar APC na jihar Kebbi, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh. Samaila Yombe Dabai, Sanata Adamu Aliero, Ministan shari'a Abubakar Malami, Sanata Muhammadu Magoro,Kakakin Majalisar dokoki na jihar Kebbi da sauran manyan baki daga ko ina a fadin jihar Kebbi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN