Yunkurin yajin aikin kanikawan mota a jihar Kebbi, Yombe ya shiga tsakani

Isyaku Garba |

Kungiyar kanikawa ta Nigerian Automobile Technicians Association NATA reshen jihar Kebbi ta kai ziyara ga Mataimakin Gwamnan Kebbi Alh. Samailla Yombe Dabai bisa gayyata ta Mataimakin Gwamnan sakamakon yajin aiki da 'yayan kungiyar suka kudiri aniyar za su yi bisa wasu dalilai na rashin jin dadi akan wasu lamura da suka shafi barayi da ke yi masu sata.

Bayanai sun nuna cewa Mataimakin Gwamna ya gayyace su ne inda ya saurari koken su.Yayin da yake jawabi, shugaban kungiyar ta jihar Kebbi Alh. Abubakar Garba Sani ya ce 'yayan kungiyar sun yi fama da biyan dukiyar mutane sakamakon sata da ake yi masu na kayakin motoci da aka kawo masu gyara wanda ya shafi sassan injin, lagireto, kapreto tayoyi da sauransu,kuma matukar hakan ya sa wasu masu motocin sukan tilasta su biyan kayakin da aka sace a motocin su.

Ya kara da cewa kungiyar ta yi assarar akalla N6m wajen biyan dukiyar mutane da aka sace a fadin jiha a bana dalili da ya sa kungiyar ta sa masu sintiri da suka yi nassarar kama wani barawo da ya zo ya saci tayoyin motoci guda biyu a lokaci daya da kapreto da sauran kayakin motocin mutane da aka kawo masu domin su gyara.

Abubakar ya kara da cewa bayan da suka kai barawon ga jami'an tsaro na NSCDC wanda suka gurfanar da shi a gaban Kotu daga bisani suka sami labari cewa kotu ta ci shi tara N10.000 ta sake shi.Sakamakon haka 'yan kungiyar suke gani ba a yi masu dadai ba.

Tawagar kanikawan ya kunshi shugaban kungiyar na jihar Kebbi Alh. Abubakar Garba Sani, Sakataren kungiyar Ibrahim Momoh, Babban dogarin tsaro na kungiyar Sarafa Abdulazeed da sauran mambobin kungiyar.

Mataimakin Gwamna Alh. Samaila Yombe ya bukaci su kwantar da hankali kuma su hakura cewa zai kai koken su ga shugaban su kuma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Abubakar Bagudu domin samun mafita a lamarin domin kiyayewa nan gaba.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN