Matasa 3 sun kashe abokinsu bayan sun daba masa wuka a wuya

Rundunar 'yansanda na jihar Bauchi ta kama wasu samari uku wadanda take zargin su da kashe wani saurayi mai suna Abdulsalami Danlami dan shekara 18 ranar 15/12.2017 da misalin karfe 9:30 na dare a unguwar Doya na birnin Bauchi.

Wadanda aka kama sun hada da Abubakar Yakubu, Suleiman Muhammed da Kamalu Kabiru.

Shi dai Abubakar Yakubu wanda shi ne ya kashe Abdulsalam ya ce ya kashe shi ne bayan ya daba masa wuka a wuya.

Bayanai sun nuna cewa akwai wasu karin samari 11 da ake zargin su da hannu a wannan kisa amma sun arce kuma 'yansanda na neman su ruwa jallo.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN