Mata ta bukaci a take ta da mota bayan ma'aikata sun kwace hajar ta na N5000

Da safiyar Juma'a wani abun tausayi ya faru a garin Calabar na jihar Cross Rivers bayan wata mata ta kwanda a karkashin wata babban motan daukan kaya inda ta bukaci direban motar ya taka ta ta mutu domin ta huta.

Hakan ya faru ne bayan Kwamishinan muhalli na jihar ta Cross Rivers yayin zagayawa domin aiki a birnin Calabar ya kama wasu masu sana'oi a gefen titi kuma ya kwashe ababen da suke sayarwa.

Sakamakon haka ne aka kwace hajar wannan matar na kusan N5000 wanda shi ne iya jarin nata, bisa wannan dalili ne matar ta fashe da kuka ta kwanta a karkashin motar da aka zuba kayakin ta kuma ta bukaci direba ya taka ta.

Bayanai sun nuna cewa daga bisani jama'a sun shawo kan ta da lallashi kafin ta yarda ta fita daga kasan motar.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN