Majalisar Wakilai ta karrama wani gurgu da ya zama Lauya da kudin bara


Majalisar Wakilai ta Najeriya ta karrama wani gurgu Mr Abdulsalam Kamaldeen Idowu wanda ya yi fice sakamakon yadda ya dauki nauyin kansa da kudin da yake samu na bara a titi har ya yi karatu a jami'a da ya sa ya zama Lauya.

Mr Abdulsalam ya sami matsala ne bayan ya kamu da cutar shan inna tun yana yaro 'dan shekara uku, daga bisani mahaifiyarsa ta rasu yayin da yake da shekara hudu ,ya sa kanshi makarantar firamare a yayin da yake da shekara takwas kuma basu da gida.

Daga kudin bara ya saye takardar jarabawar GCE A 2002, ya zauna jarabawar ta GCE da JAMB kuma aka ba shi gurbin karatu a jami'ar Lagos daga bisani ya zama Lauya.





Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN