Bayan kasancewarsa matukin jirgin sama kuma mai mallakan jiragen sama na kanshi, kuma tsohon hafsan soji mai mukamin Kanar (Colonel) a lokacin da yake aikin soji, Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh, Samaila Yombe Dabai fitaccen haziki ne a fannin kere-kere.
Wannan Sports Car mota ce da Yombe ya saya a 1981 lokacin da yake jihar California na kasar Amurka, amma kalli yadda ya sake fasalin motar zuwa mota ta zamani. Haka zalika wata mota Ford, Yombe ya sake mata fasali zuwa motar zamani ta alfarma wacce aka sake mata fasali da aka saka mata talabijin da naurar sanyi na musamman da kujeru na alfarma tamkar kana cikin dakin ka.
Akwai wata mota Armored Carrier wacce Yombe ya kera da kanshi bisa nashi fasali wanda zai iya daukan jami'an tsaro cikin tsari da kuma sauki.
Idan dai har Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi zai kasance mai saukin rayuwa da hazaka kan kere-kere duk da matsayin sa da shekarunsa, ya zama wajibi kenan matasa su tashi tsaye domin su koyi harkar fasaha domin samun madogaran rayuwa sai kuma Gwamnati ta taimaka domin abin ya bunkasa.
Daga Isyaku Garba
Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.