• Labaran yau

  Jigajigan jam'iyar APC a Kano za su gurfanar da Buhari a Kotu idan bai tsaya takara ba a 2019

  Wasu jigajigai a jam'aiyar APC mai mulki a jihrar Kano sun yi barazanar gurfanar da shugaba Muhammadu Buhari agaban Kotu matukar bai tsaya a takarar shugabancin kasa ba a shekara ta 2019.Manyan 'yan jamiyar ta APC sun yi wannan barazanar ne jiya a wani taro na 'ya'yan jam'iyar inda daga bisani suka amince da tsayar da shugaba Buhari a matsayin 'dan takara a karkashin jam'iyar APC a zabe na shugaban kasa a 2019.

  Wata sanarwa da ta fito daga wani hadimin shugaba Buhari watau Garba Shehu ,ya ce "shugaba Buhari bai karbi tayin da aka yi masa ba kuma bai ki tayin ba a cikin jawabinsa ,domin dai shugaban yayi murmushi ne inda daga bisani ya mayar da muhimmanci a kan bayanin hadin kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyar da kuma al'umomi a Najeriya ".

  Taron ya sami halarcin Gwamnan jihar Kano Ganduje ,Mataimakinsa Profesa Hafeez ,Sanatocin jihar,'yan majalisar wakilai na jihar da 'yan majalisar dokoki na juhar da sauran al'umar jaihar .

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Jigajigan jam'iyar APC a Kano za su gurfanar da Buhari a Kotu idan bai tsaya takara ba a 2019 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama