• Labaran yau

  Dalilin da ya sa Sa'idu Dakingari da hadimansa suka koma APC - Samaila Yombe

  Isyaku Garba |

  A ranar Juma'a ne tsohon Gwamnan jihar Kebbi Alh Sa'idu Nasamu Dakingari tare da wasu manyan hadimansa wadanda suka taka rawar shugabancin jihar ta Kebbi karkashin jam'iyar PDP taswon shekara takwas suka sake sheka zuwa jam'iyar APC mai mulki a Najeriya da jihar Kebbi.Wata majiya ta shaida mana cewa hakan ya faru ne tare da dimbin magoya bayan tsohon Gwamnan wanda ya zo bayan canja sheka da dubatan 'yan PDP suka yi zuwa APC 'yan watannin baya.

  Sakamakon haka ISYAKU.COM ya tambayi Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi ko miye sanadin wannan canjin sheka da 'ya'yan jam'iyar PDP ke ta yi zuwa APC a jihar Kebbi?

  Alh. Samaila Yombe Dabai ya shaida mana cewa " Godiya ta tabbata ga Allaha da ya kawo mu rana wa ta yau da tsohon Gwamna Sa'idu Dakingari da Mataimakinsa har da jama'ar sa duka sun baro PDP suka koma APC . Tuni dai Mai girma Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya bude kofa na karbar mutane a zo a hada guiwa a taimaki jihar Kebbi domin hadewa tsintsiya madaurinki daya zai tabbatar da samun ci gaba wajen taimaka wa cigaban jiha".

  Yombe ya kara da cewa "Wannan ya nuna irin kwazo da ci gaba da Gwamna a Atiku Bagudu ya kawo ma jihar Kebbi ne a cikin gajeren lokaci na shekara biyu shi ne ya burge su da ya sa suka bukaci su zo ayi wannan tafiya da su. Bayan haka Allah ya yi wa Gwamna Bagudu baiwa na salon shugabancin sanin yadda zai tafiyar da jagorancin al'umma".

  "Sau da yawa nike bayani da ambaton cewa Allah ya yi wa jihar Kebbi gata, domin Allah ya bamu adalin shugaba, kuma ai ka gani ba a boye yake ba domin dubu dubatan mutane ne ke barin waccan jam'iya suna dawowa APC saboda martaba da salon shugabancin da Allah ya ba Mai girma Gwamna Abubakar Atiku Bagudu. Ya iya shugabanci kuma haskakken mutum ne"

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Dalilin da ya sa Sa'idu Dakingari da hadimansa suka koma APC - Samaila Yombe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });