• Labaran yau

  Karanta abin da maganin basir ya yi wa mutum 4 a kauyen Ngaski

  Daga Sani Musa Saminaka da Isyaku Garba |

  Wasu matasa a kauyen Kambuwa da ke karamar hukumar Ngaski sun sami kansu cikin yanayi na damuwa sakamakon wani maganin gargajiya da suka sha daga bisani ya bugar da su. Hakan ya haifar masu da yin amai da kuma tsananin buguwa da jiri kuma yanzu haka sun kwance a yanayi na rashin sanin inda waurin da suke.

  Wakilinmu ya shaida mana cewa hakan ya faru ne bayan matasan sun karbi wani maganin gargajiya da aka ce masu yana maganin basir (dankanoma) da kuma ciwon daji.

  Bayanai sun nuna cewa sunan maganin "Kurkura" kuma wannan lokacine karo na farko da matasan suka fara amfani da maganin. Mutum hudu ne aka gani a kwance a yanayi na galabaita da rashin sanin wurin da suke.

  Likitoci dai sun sha gargadi ga yadda ake amfani da magungunan gargajiya ba bisa ka'ida ba, musamman ganin cewa wasu magungunan gargajiya basu da ka'idar yadda za'a sha sakamakon haka kuma zai iya haifar da matsala ga lafiyar mai amfani da maganin.

  Wani Likita Dr. Sani ya shaida mana cewa duk da yake maganin gargajiya yana da amfani ainun , saboda dubban shekaru da aka dauka an amfani da su, amma rashin ka'ida a wajen mu'amala da shi zai iya haifar da damuwa marmakin yayi magani.

  Ya kara da cewa ba mamaki maganin da suka sha ya zama kalubale ne ga tsarin yadda jikin su yake aiki wanda ya ce akwai bukatar nan take a garzaya da wadannan matasan zuwa Asibiti mafi kusa da su domin samun kulawar gaggawa daga Likita.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta abin da maganin basir ya yi wa mutum 4 a kauyen Ngaski Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });