Cikar Gwamna Bagudu shekara 56, Yombe ya bukaci a yi addu'a na musamman

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alh Samaila Yombe Dabai ya gode wa Sheikh Abubakar Giro Argungu bisa ziyarar ban girma da ya kawo masa a gidansa tare da tawagarsa da yammacin Talata. Yombe ya bukaci Shehun Malamin domin ya gudanar da addu'a ga Mai girma Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu sakamakon cikansa shekara 56 yau a Duniya.

Malaman sun gudanar da 'addu'a don neman Allah ya ja tsawon kwana ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ,Gwamna Atiku Bagudu da sauran al'umman Najeriya gaba daya.Sun kuma roki Allah ya kara wadata Najeriya da zaman lafiya da ci gaba.

Bayan gudanar da addu'a, Sheikh Giro ya ce sun zo ne domin sada zumunci ta ziyarar ban girma ga mataimakin Gwamna.

Daga cikin tawagar Sheikh Abubakar Giro sun hada da Mal. Ibrahim Bayawa, Alaramma Suru da sauran Malamai

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN