Dubun 'yan fashi da makami da ke amfani da kakin 'yansanda ya cika

Rundunar 'yansanda na jihar Enugu sun damke wasu 'yan fashi da makami da ke addabar matafiya a kan hanyar Lagos zuwa Benue sakamakon bukukuwan Kirsimeti kafin 'yan sanda su kai masu farmaki a kwanar Mil 9 da ke wajen garin Enugu ranar Lahadi.

An kama mutum 4 sanye da tufafin 'yansanda yayin da biyu suka tsere da raunukan harsashi. An kama 'yan fashin da bindigogi guda uku kirar hannu da wayayoyin salula guda tara.

Mai magana da yawun hukumar 'yansanda na jihar Enugu SP Ebere Amaraizu ya ce an yi nassarar cafke batagarin ne sakamakon bayanan sirri da suka samu wanda nan take 'yansanda na sashen runduna ta Mil 9 suka kai samame da ya kai ga kama 'yan fashin.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN