• Labaran yau

  Mubi: Tashin bom a masallaci ya kashe mutum 50 lokacin sallar asuba

  Akalla mutum 50 ne ake fargaban sun mutu sakamakon fashewar bom da aka tayar a  wani Masallaci da ake kira Madina a birnin Mubi na jihar Adamawa.'Dan kunar bakin waken ya tayar da bom din da ke a jikin sa yayin da aka tayar da Sallar Asuba da yake cikin sahu a tsakiyar jama'a a cikin Masallacin ranar Talata.

  Rahotanni sun nuna cewa rundunar 'yansanda ta jihar Adamawa ta tabbatar da faruwar lamarin.

  Amma Kwamishinan watsa labarai na jihar Adamawa Ahmed Soja ya ce a halin yanzu basu gama tantance iya adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

  Ya kara da cewa da yawa daga cikin mutanen da abin ya rutsa da su gabobin jikinsu sun tarwatse, saboda haka zai yi wuya a gane adadinsu.

  Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ta tura ma'aikatan kiwon lafiya garin na Mubi domin yi wa wadanda lamarin ya shafa magani na gaggawa da kuma ceton rayuka.

  Wannan ne karon farko da aka kai hari da ya kai haka muni garin na Mubi, tun bayan sojojijn Najeriya sun kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram
  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mubi: Tashin bom a masallaci ya kashe mutum 50 lokacin sallar asuba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });