• Labaran yau

  Kebbi: Matar aure ta yi batan dabo a garin Saminaka a karamar hukumar Shanga

  Daga Sani Musa Saminaka |

  Wata mata ta bar gidan mijinta da sunan zata je sayen Masara a wani gida yau kusan wata daya kenan ba ita kuma babu labarin ta, an bincika duk inda ake sa ran ta je, amma har yanzu ba labari.

  Ita dai wannan yarinyar tana da Aure kuma tana dauke da jaririya wacce ke shan nono .

  wannan lamarin dai yayi matukar gir-giza mutane musamman a irin yadda na zanta da mijinta da kuma daya daga cikin iyayen ta a nan cikin garin Saminaka. Na tambayi daya daga cikin ubannin ta, cewa ko menene dalilin faruwar hakan?

  Ya tabbatar mini da cewa su ma dai wannan lamarin ya firgita su matuka. Kuma gwargwado sun yi iya nasu bincike amma har yanzu Allah bai sa suka gan ta ba . Amma kuma ya nuna mini akwai alamomin da ke bayyana gareta masu nuna tana da matsalar Jinnu.

  Da wannan suke addu'a da fatar duk wanda Allah ya sa ya gan ta don Allah ya taimaka ya kira wannan Lambar 08138414197.

  Ita dai wannan yarinyar sunan ta Hajara a cikin garin Saminaka take,kuma shekarun ta basu wuce 25-28 ba,amma asali cikin garin Keri take , Saminaka zuwa akayi da ita.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kebbi: Matar aure ta yi batan dabo a garin Saminaka a karamar hukumar Shanga Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });