• Labaran yau

  'Dan shekara 65 da ya sace yaro ya yi masa fyade tsawon shekara 1

  An kama wani mutum mai suna Patrick Kalu wanda ake zarginsa da sace wani yaro 'dan shekara 15 kuma ya dinga yi masa fyade har tsawon shekara daya a jihar Neja.

  Patrick uban yara uku ne kuma 'dan asalin Ohafia na jihar Abia yana zaune ne a unguwar rukunin gidajen railway a garin Minna.

  Bayanai sun nuna cewa ana zargin Patrick da yin lalata da yara masu kimanin shekara 12 zuwa 15.

  Mai magana da yawun hukumar 'yansanda na jihar Neja Abigail Unaeze ya tabbatar da faruwar lamarin ya kara da cewa rundunar za ta gurfanar da Patrick a gaban Kotu da zarar an kammala bincike.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: 'Dan shekara 65 da ya sace yaro ya yi masa fyade tsawon shekara 1 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama