• Labaran yau

  Soji sun kifar da Gwamnatin shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe

  Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun nuna cewa Sojin kasar sun kifar da Gwamnatin shugaba Robert Mugabe na jam'iyar Zanu PF a daren Talata bayan an ji karar fashe-fashen ababe da ake dangantawa da igwa kuma daga bisani aka ji karan harbin bindigogi a Harare babban birnin kasar.

  Shugaban kasar Afrika ta kudu Jecob Zuma ya ce shugaba Robert Mugabe ya shaida masa ta wayar tarho cewa yana tsare a gidansa kuma yana cikin koshin lafiya.

  Wata majiya ta labarta cewa Mugabe ya bukaci a bar Matarsa Grace ta fice lafiya kalau zuwa kasar Afrika ta kudu.Wannan juyin mulkin Soja shi ya kawo kashen mulkin shugaba Robert Mugabe na tsawon shekara 37 a kasar.

  Mr Jecob Zuma na Africa ta kudu ya bukaci a kwantar da hankali kuma a kai zuciya nesa a kasar ta Zimbabwe kuma ya bukaci rundunar Sojin kasar su bi a sannu.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Soji sun kifar da Gwamnatin shugaba Robert Mugabe na kasar Zimbabwe Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });