'yansanda sun kama Soja 4 da wasu mutum 7 bisa zargin satar bututun karfe

'Yansanda a garin Lagos sun kama wasu sojin sama guda hudu tare da wasu mutum bakwai na Ma'aikatan Albarkatun Ruwa na jihar Lagos bisa zargin su da satan bututun ruwa na karfe da kudinsu ya kai kimanin Naira Miliyan 25 a wani samame da suka kai ranar Litinin.


The Nation ta ruwaito cewa sojin saman Air Crew Men (ACM) Akingbola Wole, Ugbong Abel, Alalifu George da Kumish Revelation wanda suna aiki ne tare da Rundunar Sojin Sama ta 055 NAF Camp, Victoria Island,an kama su ne yayin da suke bayar da kariya ga masu satan bututun ruwan  ranar Asabar da safe misalin 11:30.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Lagos Imohimi Edgal ya shaida wa manema labarai cewa za'a gabatar da wadanda ake zargin a gaban Kotu yayin da aka mika Sojojin ga Kwamandan rundunar sojin sama ta 055 NAF domin fuskantar hukunci na Soji.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN