Yadda Facebook da Whatsapp ke shafan rayuwar Bahaushe -- Bincike

Facebook,Twitter,instagram da Whatsapp shafukan sada zumunta ne da bature ya kirkiro domin nishadantarwa da sada zumunta.Amma yanayi da aka karkata manufa da amfani da wadannan shafukan ya banbanta daga nahiya zuwa nahiya,addini,zamantakewa ko al'umma.

A nan kasar Hausa,Facebook ya zama wajen tsegumi, yada farfaganda na siyasa ko addini da dai sauransu.

Wani bincike da ISYAKU.COM ya gudanar na tsawon wata uku ya nuna cewa a cikin samari 30 a kasar Hausa 15 sukan shiga shafin Facebook ko Whatsapp akalla sau 10 a rana domin su bincika lamarin da ke tafe a shafukan saboda kada a bar su a baya.

Haka zalika binciken ya nuna cewa cikin samarin guda 10 guda 3 ne a cikin su ke ziyartar Alkur'ani ko wadda ake da ita a cikin wayar salula ko ainihin rubutaccen Alkur'ani domin karantawa akalla sau daya a rana.

A bangaren yanar gizo kuwa binciken ya nuna cewa al'umman Hausa su ne wadanda basu amfana ba sosai da harkar yanar gizo kasancewa kusan a samari 50 akalla 30 suna cikin Facebook ko Whatsapp amma akalla mutum 1 ne a cikin mutum 100 ke amfana ta hanyar yin wani karatu wadda ake samarwa kyauta a shafukan yanar gizo saboda su inganta rayuwarsu sabanin yadda 'yan kudancin Najeriya ke yawan yin karance karance ta shafukan yanar gizo misali jihar Ogun ,Oshun ,Ondo, Enugu,Bayelsa da saransu da ke da akalla mutum 15 daga cikin  mutum 100 da ke yin karatu ta yanar gizo.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN