Wani jirgin ruwa ya sake nutsewa a Yauri

A Yauri wani jirgin ruwa kwale kwale ya nutse ranar Alhamis sakamakon bugun taguwar ruwa mai karfin gaske da ya zama musabbabin nutsewar.

Wakilanmu na kasar Yauri da kewaye sun shaida mana cewa daga farko dai ganin yadda taguwa ke bugawa da karfin gaske,jami'an tsaro da ke Mashayar kasabo sun gargadi matuka jirage akan kada su shiga ruwan da jirgi har sai bugun taguwar ya rage.A wani abin da za'a iya cewa yin biris ne da umarnin jami'an tsaro ,wasu matuka jirgi sun yi awon gabansu suka ci gaba da harkarsu kuma daga bisani wannan ibtila'in ya auku.

Wakilanmu sun labarta mana cewa akwai mutum 4 da ake zargin cewa suna cikin jirgin amma ba'a gansu ba har yanzu bayan aukuwar lamarin wadda ake harsahen cewa jirgin na dauke da akalla mutum 30 bayan buhuhuwan masara da sauran amfanin gona da suka salwanta.

Daga sani Twoeffect Yawuri da Sani Musa Saminaka

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN