Soji sun ceto 'dan shekara 5 daga hannun 'yan boko haram

Sojin Najeriya da ke fada da 'yan kungiyar boko haram sun ceto wani yaro 'dan shekara 5 daga hannun 'yan kungiyar boko haram a wani fada da aka gwabza tsakanin Sojin da 'yan kungiyar ta BH a karamar hukumar Bama.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya Brig. Gen. Sani Kukasheka Usman ya shaida wa manema labarai ranar Juma'a cewa dakarun rundunar sojin Bataliya ta 202 da Brigade ta 21 karkashin shirin operation lafiya dole sun yi artabu da 'yan kungiyar ta BH inda dakarun Soji suka yi nassarar kora tare da kakkabe  'yan kungiyar a kauyukan Abaram, Churuchuru da Aulajirina.

An kama wasu makamai daga hannun 'yan kungiyar yayin da wasu suka ranta na kare da raunukan harsashi.


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN