Barawo ya sace N6.5m da aka boye a karkashin gado

Barayi sun sace kudin wata mata mai suna Esther kimanin N6.5 Miliyan wadda ta boye a cikin wata jakar Ghana must go a karkashin gadon ta a unguwar Ajah da ke garin Lagos.

Esther ta lura cewa kudin ta sun bace bayan bata gan jakar ta ba da ta boye  a karkashin gado makare da kudin.Sakamakon haka ta kai kara a ofishin 'yansanda.

Jami'an 'yansanda sun kama wani da Esther take zargi kuma matashin mai suna Okoronkwo bai dade da sayen wata mota kirar SUV ba lamarin da ya ba kowa mamaki domin ba da dadewa ba Okoronkwo yakan roki mazauna unguwar domin ya sami kudin da zai ci abinci.

Kasancewa Okoronkwo ya yi arziki a dare daya ya haifar da zargi akan lamarinsa domin baya wani aiki da zai tabbatar da sahihancin sanadin da ya kaishi ga mallakar dukiya a dare daya.

Bayan jami'an 'yansanda sun gudanar da bincike,Okoronkwo ya amsa cewa tabbas ya sato kudin ne a karkashin gadon Esther lokacin da ta tafi aiki.

An gabatar da Okoronkwo gaban Kotun Majistare bisa zargin sata.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN