Shekara 20 na rashin karin girma,Ganduroba ya maka hukumar gidan yari a Kotu

Wani jami'in rundunar gidajen yari na Najeriya a jihar Imo Longinus Njoku ya maka rundunar a wani Kotu na musamman bisa zargin danne masa hakki ta hanyar hana shi karin girma har tsawon shekara 20.

Longinus ya shaida wa Kotun cewa a tsawon shekara 32 da ya share yana yi wa hukumar aiki, bai taba aikata wani laifi ko aikata wani kuskure ba amma haka kawai hukumar ta tauye masa damar samun karin girma ba tare da wani dalili ba.

Ya kuma kara da cewa yana bukatar Kotun ta tilasta hukumar gidajen yari ta kasa ta biya shi Naira Miliyan 20 zaman hakkinsa da kuma hali na wahala ta damuwa da hakan ya jawo masa.Daga cikin shekaru da aka hana shi karin girma sun hada da 1999, 2002, 2005, 2008, 2001 da 2014.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN