• Labaran yau

  Gwamnati za ta kwace kudaden asusun banki da basu da lambar BVN

  Gwamnatin tarayya ta hannun Ministan shari'a Abubakar Malami ta bukaci Kotu ta bayar da dama domin ta kwace kudaden asusun ajiyar Banki wadanda basu da lambar BVN.

  Hakan ya biyo bayan wani kara da Ministan ya shigar inda yake bukatar Kotun ta bayar da izini akan bukar kwace kudi a asusun kowane banki da baida lambar shaidar BVN. Sakamakon haka babban Kotun tarraya ta Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi aka bukatar ta Ministan na shari'a Abubakar Malami ranar 17 ga watan Oktoba.

  Haka zalika Kotun ta bukaci Bankuna su yi bayani akan dalilai da zasu sa kada a aiwatar da dokar cikin kwanaki 14.

  Yanzu haka Bankuna na bari a ajiye kudade a asusun da basu da BVN amma basu bari a cire kudi daga irin wadannan asusun.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamnati za ta kwace kudaden asusun banki da basu da lambar BVN Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });