Sarkin Musulmi yayi wannan jawabi ne a wajen taro na 9 domin mutunta darajar 'dan adam a jami'ar Najeriya da ke Nsukka.
Basaraken yace wadanda ke kashe mutane tare da tunanin cewa suna yin aikin Allah ne suna yaudaran kansu ne domin Allah baya lamuntar zubar da jinin bil'adama ko da ba Musulmi bane.
Haka zalika Sultan Abubakar yace duk wata al'umma da bata mutunta rayuwar dan'adam ba al'umma ce da ta waye ba.Ya kuma kara da cewa babu yadda Fulani makiyayi zai kashe dan adam domin ya kare ran shanu,saboda haka masu aikata laifi ne ke kashe mutane amma ba Makiyaya masu kiwon shanu ba.
Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Tags:
LABARI