Ko ka san matasa suna yin ingantattun takalma a jihar Kebbi ?

Daga Isyaku Garba - Birnin kebbi |
Baya ga harkar noma da jihar Kebbi ta shahara a kai wacce ta kawo kudade da arziki a aljuhun mutane manoma shinkafa a fadin jihar, haka zalika Gwamnati ta dukufa wajen ganin ta iganta rayuwar Matasan domin ganin sun sami sana'an yi wacce za ta zama madogara ga rayuwarsu.

Bisa wannan tsari cibiyar fasahar koyar da ayyukan hannu a jihar Kebbi wacce ake kira Technology Incubation Centre wadda ke hanyar Kalgo dai dai kofar shiga Birnin kebbi daga hanyar ta Kalgo tana horar da Matasa ayyukan hannu kala kala.

Daga cikin akwai aikin takalma, walda, dinki, harkar kwamputa da sauransu.

Wadannan takalma a wannan cibiyar ake yin su kuma ana sayar da su da rahusa duk da ingancin kayakin da aka hada takalman da su wadda daki-bari ne.Wadannan takalma sun zama kirar jihar Kebbi kenan watau Made in Kebbi.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN