B-kebbi: 'Yan shi'a sun gudanar da tattakin Ashura a jihar Kebbi (Hotuna)

Da safiyar yau mabiya Shi'a suka gudanar da tattaki da ya bi da su ta kan wasu mahimman hanyoyi a cikin garin Birnin kebbi wadda ya sami halartar daruruwan maza da mata mabiya wannaan tafiyar da suka ce ana gudanar da shi yanzu haka a fadin Duniya ba wai a Najeriya kadai ba.

Mal Umar Makerar Gandu wadda jigo ne a cikin mabiya fahimta ta Shi'a a jihar Kebbi yayi bayani cewa a kowane shekara 'yan Shi'a suna gudanar da wannan tattaki domin tunawa da kisan gilla da akayi wa Imam Hussain a 10 ga watan Muharram kuma shine dalili da ya sa suka gudanar da tattaki na yau.

Mal Umar ya yi kira ga wadanda ke jifansu da kalamai da ya kira "kazafi ,karya da jita jita" cewa su dinga bincike kafin su furta kalamai don neman su bata sunan Shi'a alhalin Shi'a bata bata sunan kungiyar addinin kowaba face fahimtar da Musulmi muhimmancin hadin kai da zumunci.



Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN