• Labaran yau

  An kashe matashi bisa zargin kasancewa mai shan jinin bil'adama

  An kashe wani matashi kuma aka kone gawarsa bayan an zargeshi da kasancewa cikin masu shan jinin bil'adama watau vampire a kusa da Blantyre babban birnin kasar Malawi.

  Wani 'dan Jarida Lucy Ashton yace an gano mutumin wanda ake zargin cewa yana fama da cutar farfadiya a gefen wata Makabarta da dare kuma aka kaishi caji ofis na 'yansanda ranar Alhamis.Alamu sun nuna cewa watakila mutumin yana kan hanyarsa ce ta dawowa daga Asibiti domin an sami katin Asibiti a tare da shi.

  Daga bisani wasu mutane suka baza jita-jita a cewa an kai wani mai shan jinin mutane caji ofis lamarin da ya sa jama'a suka yi cincirindo a ofishin na 'yansanda suka jawo mutumin da karfin tsiya suka kashe shi kuma suka kone shi.

  Wannan shine mutum na uku da aka aiwatar masa da irin wannan 'danyen hukunci da 'dan jaridar ya kira hukuncin jahiliyya a kasa da watanni uku a Malawi bisa zargin kasancewa masu shan jini ne.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: An kashe matashi bisa zargin kasancewa mai shan jinin bil'adama Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });