Bincike - Ababen da ke sa mutum ya kashe kan shi

19.Oct.2017 Isyaku Garba

Mutane kan yi mamaki idan ance mutum ya kashe kansa, mace ko na miji yaro, babba ko tsoho kuma lamari ne da ke kasancewa a ko wane irin jinsi na bil'adama.Mi ke kawo tunanin mutum ya dauki ransa da kansa ?.

Sakamakon wani bincike da na gudanar kan lamarin ya nuna cewa ba kasafai mutum zai dauki ransa ba sai da wasu dalilai da ya dade yana fama da su ko da ya shaida wa wasu ko kuma yayi fama da lamarin da ya boye a zuciyarsa shi kadai.

Ababe da za'a fara kula ga mai tunani da zai iya kaiwa ga kashe kansa:

Da farko dai yawan magana game da yiwuwar kashe kai, mutum idan yana yawan wannan zancen yana da kyau a bashi kulawa ta musamman. Mafi yawa za ka kula da cewa yana fama da matsanancin damuwa.

Fiye da kashi 90 na wadanda suka kashe kansu sun kasance masu shan barasa ko amfani da kwayoyi har watakila sukan yi amfani da ababe masu gusar da hankali kamar yadda sakamakon binciken WMDs ya nuna.Haka zalika sukan kasance masu fama da wata matsalar rashin lafiya mai tasani ko cuta da bata da magani.

Ababen da ya kamata a kula da zasu iya sa mutum ya kashe kansa:

1. Kasancewa mutum ya taba yunkurin kashe kansa
2. Tarihin zuriya ko akwai mai tabin hankali ko shaye shaye
3. Ko da akwai wanda ya taba kashe kansa a zuriya
4. Tarihin mumunar tashin hankali a zuriya
5. Takurawa mai tsanani ko fyade
6. Ajiye makami a gida
7. Matsanancin ciwo bayyananne
8. Wariya ko tsarewa na gallazawa da cin zarafi
9. Yawan bincike ko karanta bayanai yadda wasu suka kashe kansu cikin sauki

Alamomi da ke iya nuna cewa mutum zai kashe kansa:

1. Yawan magana akan mutuwa
2. Matsanancin rashin lafiya da ba'a warkewa, matsanancin bakin ciki, rashin iya barci ko cin abinci da ya wuce kima sakamako damuwa.
3. Yi ma kai fatar mutuwa
4. Rashin jin dadin ababen da ake jin dadinsu a baya
5. Yawan magana akan rashin jin dadi, kasancewa baka da amfani a rayuwa, Duniya ta ki ka, babu mai taimakon ka da sauransu.
6. Yawan cewa "rayuwata bata da wani amfani , ko da ma ba'a halicce ni ba" da sauran su.
7. Kasancewa cikin farin ciki farat daya alhali mutum yana cikin mumuna da matsanancin damuwa.
8. Yawan furuci akan cewa "ni fa zan kashe kaina in huta"
9. Kiran mutane kayi bankwana da su ko ta hanyar ziyara ko sako ko a wayar salula.


Matsawar ka kula da wadannan ababe da na zana a sama kuma ka san cewa mutumin da ke nuna wadannan alamaomin yana cikin matsanancin damuwa , to yana da kyau a kusanceshi domin a shawo kan lamarin da yake  cikin zuciyarsa kamar yadda akasarin irin wadannan mutan sukan boye damuwarsu hatta sai ya kai matsayin da lamari ya gagara.

Daga Isyaku Garba

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN