Wasu Nurse 5 sun bude jakar gawa domin su gan girman al'auran mataccen

Hukumomi a Asibitin  Denver Health Medical sun dakatar da wasu Mata masu aikin jinya a Asibitin su biyar (Nurse) sakamakon samun su da laifi bayan sun buda wajen da aka ajiye gawar wani mutum da ya mutu a Asibitin domin su gan girman al'auransa.

Sashen rundunar 'yan sanda na Denver ta kaddamar da bincike akan lamarin amma daga bisani aka mayar da zancen a karkashin hukumar Asibitin domin aiwatar da hukunci na cikin gida a karkashin dokokin Asibitin.

Daga bisani Hukumomin Asibitin sun dakatar da Nurse din su biyar har tsawon Makonni uku domin ya zama darasi ga saura.

Wata mace ma'aikaciyar Asibitin ce ta jiyo 'yan matan su biyar suna tattaunawa akan lamarin wadda ita kuma ta gan cewa hakan ba daidai bane saboda haka ta tafi ta shaida wa hukumomin Asibitin.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN