"Shugaba Buhari ba zai tsaya takara ba a 2019" - Aisha Alhassan

Ministan harkokin mata a Najeriya Aisha Alhassan ta ce shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa 'ya'yan jam'iyar APC a 2015 cewa "ba zai sake tsayawa takara ba idan an zabeshi domin yana son ya gyara barnar da PDP tayi ne a gurbi daya na mulkinsa".

Minisatan ta fadi haka ne a wata hira da tayi da Reuters. Wannan ya biyo bayan wata hira da tayi da BBCHausa inda ministan ta ce zata goyi  bayan Atiku Abubakar matukar ya fito takara a zabe na 2019 kuma ba zata yi nadama ba ko da Shugaba Buhari ya sallame ta daga mukaminta na Minista sakamakon kalaman da ta yi.

Amma da yawa daga cikin mutane musamman 'yan Arewacin Najeriya suna ta tofa albarkacin bakinsu akan lamarin musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

Mal.Yunusa Zuru wani mai fashin baki ne a harkar Siyasa ya shaida wa ISYAKU.COM cewa "abinda wannan matar ta yi ba komai bane face Allah ne ya fara bayyana butulai da mutane masu manufar boye da kuma makiya Shugaba Buhari da suke tare da shi amma basa sonsa"

Yunusa ya kuma kara da cewa "Lokaci yayi da Buhari zai yi motsi mai karfi domin ya jijjige munafukai daga cikin tsarin tafiyarsa kafin su illata manufarsa ta alhairi ga 'yan Najeriya".

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN