B-Kebbi: Na fita daga kungiyar HADTECH sakamakon rashin ragowa - Isyaku Garba

Daga yau Lahadi 10/9/2017 ni Isyaku Garba ina sanar da duk wanda wannan lamarin ya shafa cewa ban cikin kungiyar masu gyara da sayar da waya mai suna HADTECH sakamakon halaye na rashin ragowa ,da cin mutunci gareni da sunan kungiya .

Idan baku manta ba,ni Isyaku Garba na kirkiro HADTECH a 2013,na rada mata suna HADTECH kuma na fara tafiyar da mataki domin ayi wa kungiyar rijistarta a CAC kafin a sami bullowar cin zarafi da rashin ragowa da ya sa wasu da ke tunanin cewa su wasu abu ne a nasu tunani suka ci zarafi na ta hanyar nada wani mai tunani irin nasu cewa shi ne shugabansu.

An roke da cewa in yi hakuri bayan an kasa bayar da hujjoji ko dalilai da suka sa aka yi nadi alhalin akwai wadda jama'a suka wakilta a waccan lokaci amma babu bayani mai gamsarwa.

Nayi hakuri a bisa dalilin cewa daga baya na fahimci cewa yadda na yi zaton kimar wasu ba haka abin yake ba saboda tun asali TAMKAR mu ba daya bace.

Shekara hudu tun wannan nadin babu ci gaba a zahiri balle ayi tunanin nassara ,face cin mutunci,rashin ragowa da kumbura baki na iska da babu amfani.Haka zalika jahilci da ,girman kai bazai yiwu ya zama ado ba a tafiya ta mutane masu ilimin son ci gaba da yayi daidai da zamani ba.

Lokacin da na shigo gidan harkar gyaran waya a Birnin kebbi a matsayin kwararre a fannen ingizon mobile phone software & schematics na sami wasu mutane a wani wuri,bayan wasu shekaru na yi karatun koyon aikin jarida sakamakon da yasa na buda shafukan isyaku.com da kebbi24.com wadda kamfanina na Seniora Tech ke tafiyar da su domin jama'a .Amma wajen da na sami wasu a shekarun baya a nan suke har yanzu, dalili da ya sa dole a sami banbancin fahimta domin ni ina son ci gaban jama'a,jihar Kebbi da kasata Najeriya ba wai a dinga ce mani ciyaman ina tinkaho na jeka nayi ka ba.

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN