"Duniya za ta zo karshe ranar Asabar 23, Satumba" - Pasto masani Taurari

Wasu Malaman Choci masana lissafin taurari sun yi harsashen cewa Duniya zata tashi ranar Asabar mai zuwa 23,Satumba 2017.Masanan sun kafa hujjarsu daga littafin injila (Bible) sura ta Luke 21: 25 zuwa 26 wadda ke bayani cewa "Duniya ta zo karshe".

Masana taurarin na addinin Kirista sun ce kididdiga  daga Injila sun yi daidai da ranar 21 ga watan Agusta ranar da Rana ta kama Wata a kasar Amurka da ranar 25 ga watan Agusta ranar da mahaukaciyar guguwar Harvey ta auku sai ranar 26 ga watan Agusta ranar da mumunar ambaliyar ruwa sakamakon guguwar Harvey ta mamaye garuruwan Houston da Texas.

Sun kuma kara da cewa dawowar Annabi Isah AS kamar yadda ya ke a Injila yana nufin "wata mata zata fara baiyana da sutura ta Rana da Wata a karkashin kafafuwanta da kuma wata hular sarauta mai Wata guda goma sha biyu" .

Malaman sun ce wannan Matar ana nufin tauraruwar Virgo ce kuma mako mai zuwa Rana da Wata zasu kasance a Virgo haka ma tauraruwar Jupitar wadda take nufin Annabi Isah AS.

Irin wannan yana faruwa kowane shekara  12,sun kara da cewa wani daidaitar Taurari da Duniya wadda ake kira “the Lion of the tribe of Judah” zai faru a wannan lokacin.

Jagoran kirkiro wannan tunani mai suna David Meade ya yi harsashen cewa wani dunkulallen dutse mai girma watau Planet X, ko kuma Nibru zai bayyana a sararin samaniyya , ya ce wucewar wannan dutsen kusa ko ma yayi karo da Duniyar mu shi ne zai haifar da guguwar farkon kasancewa karshen Duniya wadda zai faru a ranar 23 ga watan Satumba kamar yadda ya samo hujja daga lissafin Injila (Bible) da kuma makin ranaku na tarihi daga Dalar kaburan Sarakuna a Giza na kasar Masar (Egypt).

Amma hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA ta ce wannan shaci fadi ne kawai domin babu wata hujjan kimiyya da ta tabbatar da haka.

Wannan harsashen na David Meades Chocin Roman Catholic, Protestant, Anglican ko Orthodox basu gamsu ko tantance sahihancinsa ba.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN