B-kebbi - Ziyarar V.I.O wajen 'yan sanda, ababen da ya kamata ka sani

A yau ne babban darakta na kula da ababen hawa na jihar Kebbi wadda aka fi sani da V.I.O Lawal Hamisu Gulma tare da tawagar hafsoshin rundunarsa suka kai ziyarar aiki a ofishin DPO na 'yansanda a garin Birnin kebbi.

Darakta Gulma ya shida wa ISYAKU.COM cewa ziyarar tasu a yau ziyarace da aka saba daga lokaci zuwa lokaci domin karfafa fahimta na aiki tsakanin bangarorin wajen tafiyar da aikinsu.

Ya kuma kara da cewa "Mun tattauna game da abubuwan hawa da masu abubuwan hawa da kuma shawarwari akan irin ababen hawa da ya kamata su hau hanya da irin ababen da mutane ya kamata su sani  kafin su fara tuki a kan hanya".

"Masu ababen hawa sunyi yawa wasu basu san ka'idodin tuki ba shi yasa muke yin kokari muyi yawo mu yi fadakarwa mu kuma tunatar da mutane su san dokokin hanya domin kariyar lafiyarsu da dukiyoyinsu a kasarnan.Shiri ne da muka fara daga kananan hukumomi tare da abokan aikin mu".

Kwamandan ya yi karin haske yadda mai tafiya a kafa ya kamata ya yi akan hanya inda yace "Mai tafiya a kasa ya kamat ya fuskanci abinda ke tafe ba wai ya ba ta baya ba kuma idan dare ne akwai irin tufafin da ya kamata ya saka domin mai abun hawa ya hango ka ma'ana tufafi mai haske.Kuma a kowane lokaci mai tafiya a kasa ya dinga fuskantar mota ko babur da ke gabanshi ba wai ya basu baya ba wadannan sune ababe guda biyu da ya kamata mai tafiya a kasa ya sani masu muhimmanci".

Daga karshe yayi kira ga masu ababen hawa cewa su bi doka da oda sa'annan a zauna lafiya.


Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN