An kama 'yan IPOB 2 da suka kashe Hausawa 4 a Abraka jihar Rivers

Rundunar 'yansanda na jihar Rivers ta kama mutum biyu da ta ce sune suka kai hari da yayi sanadin mutuwar Hausawa 4 a Abraka ranar Juma'a da dare.

Mutanen da aka kama 'yan kungiyar 'yan ta'addan nan ce ta IPOB,wadda ta dukufa a 'yan kwanakinnan wajen zafafa tashe tashen hankali da yayi sanadin salwantar rayuka da dukiya mai yawa.

Bayanai sun nuna cewa na uku daga cikin wadanda aka kama ya ranta na kare.

Wadanda aka kashe sun hada da Usman Abdullahi dan shekara 45, Ali Sidi dan shekara 70, Ibrahim Zubairu dan shekara 30 da wata mata mai suna  Hauwa 'yar shekara 22.

'Yan kungiyar IPOB da aka kama sun hada da matashi dan shekara 24 Abraham Ndudi daga Kwale a jihar Delta da dan shekara 21 Okereke Ifeanyi daga Ogbaru na jihar Anambra.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda na jihar Delta DSP Andrew Aniamaka ya tabbatar da faruwar lamarin yayinda ya ce hukumar tana neman na uku daga cikin wadanda ake zargi wadda akayi wa lakabi da "Last Burial".

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN