'Yan bindiga sun kashe dansanda da farin hula a harin Choci

'Yan bindiga dadi sun kai hari a  Assemblies of God Church da ke kan titin Oguta a garin Onitsha na jihar Anambra lamarin da yayi sanadin mutuwar wani jami'in dan sanda da farin hula daya da safiyar yau Lahadi 13/8/2017.

Wannan ya farune bayan kwana 7 da faruwar irin wannan ta'addanci bayan wasu 'yan bindiga sun bindige kimanin mutum 13 tare da jikata wasu mutum 27 a wani Choci a garin Ozubulu.

Kwamishinan 'yansanda na jihar Anambra Mr. Garba Umar ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya shaida wa 'yan jarida cewa maharan sun arce da bindigar dan sanda da suka kashe amma yace rundunarsa tana bincike da zai kai ga damke wadanda suka aikata wannan ta'addanci.Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN