"PDP ta kasa a cikin shekara 16 da ta mulki Najeriya" - Sani Dododo

Dangane da kalaman da Sakataren jam'iyar adawa ta Najeriya ya furta a yayin babban taron 'yayan jam'iyar da ba'a zaba ba a ranar Asabar a Abuja inda ya ce APC ta ruguje tsarin da PDP tayi na shekara 16 wa 'yan Najeriya.Mai magana da yawun jamiyar APC na jihar Kebbi Alh.Sani Dododo ya yi raddi kan kalaman na Obi. Dododo ya shaida mana cewa da farko dai babu adalci a kalaman Obi domin me yasa PDP bata fitar da 'yan Najeriya daga kangin talauci na yunwa da fatara ba a cikin shekara 16?.

Ya kuma kara da cewa me yasa PDP a shekara 16  da tayi tana mulkin Najeriya bata inganta rayuwar 'yan Najeriya ba sai a shekara 2 kawai da APC tayi tana mulki ita PDP zata fara yin hisabi akan APC ?

Ya kuma kara da cewa PDP ta manta da yadda ta bar Najeriya cikin yunwa,talauci,rashin tsaro tashin hankali ga kuma cin hanci da rashawa?...haka PDP ta kasa tabuka komai akan tsaro musamman a yankin Borno da Adamawa da sauransu a mulkinta na shekara 16,amma APC ta mayar da kwanciyar hankali da tsaro a yankin a cikin sekara 2 kacal.

Dododo ya kara da cewa "yanzu zancen boko haram ya zama tarihi saidai abinda ba'a rasa ba,haka zalika ai gwamnatin APC ta samar da ayyuka da dama da tsare tsare kamar NPOWER da ta samar wa dubannin 'yan Najeriya aikin yi wadda suke karban fiye da N30.000 a kowane wata kuma yaya zaka iya gyara barna da aka yi a cikin shekara 16 cin shekara 2?...idan mai magana ya zama mahaukaci ai mai sauraro sai ya zama mai hankali".


Ku biyo mu a https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN