Diya ta kai iyaye kara Kotu don sun haife ta mumuna,tana neman diyyar dala miliyan 2

Wata mata a jihar California na kasar Amurka mai suna  Annabelle Jefferson 'yar shekara 44 ta kai iyayenta Robert Jefferson dan shekara 82 da Ruby Jefferson 'yar shekara 76 kara a Kotu  bisa tuhumar cewa sune suke da hakki akan  sun haife ta da munin gaske kuma tana neman Kotu ta tilasta iyayen nata su biya ta dala miliyan 2 ($2 million) saboda sun haifeta mummuna ba kyakkyawa ba.

Annabelle ta kara da cewa "sau uku aurena yana mutuwa a dalilai da aka alakanta da munina kuma ba zan lamunci wannan yanayi  ba saboda tun asali iyayena munana ne kuma shine dalili da ya sa suka haife ni mummuna lamarinda ya jefa ni cikin yanayi da nike ji kamar na kashe kaina domin bani da masoya don muni na da ya samo asali daga munin iyayena".

Ta kuma kara da cewa zata nemi hukumomi a jihar na California su yi wata doka da zata hana munanan mutane haihuwa saboda kada su haifi munanan yara da zasu yi fama da kadaici da kuncin rayuwa kamarta.


Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.s

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN