• Labaran yau

  Safeton 'dansanda ya kashe DCO akan cin hancin N150.000

  An sami rudani da tashin hankali a wani lamari da ya auku a chaji ofis na 'yansanda a Kajola na karamar hukumar Odigbo a jihar Ondo inda wani safeton 'yansanda Abraham Arowogun ya bindige wani hafsan 'yansanda Timothy Arueli har lahira a cikin ofishinsa.

  Bayanai sun nuna cewa Timothy Arueli wadda shine hafsa mai kula  da laifuka na ofishin watau DCO ya gano cewa safeto Abraham ya karbi cin hanci har na N150,000 daga hannun wani da ake bincike a kanshi kuma DCO Timothy ya umarci safeto Abraham ya mayar da kudin ga wadanda ya karbi kudin a hannunsu lamarin da ya kawo zazzafar muhawwara da yasa safeto Abraham ya fice daga ofishin DCO Timothy a fusace.

  Preium Times ta ruwaito cewa daga bisani sai safeto Abraham ya dawo da bindiga kuma bai yi  wata wata ba sai ya harbe DCO Timothy har lahira.Ganin cewa ya aikata kisa da lallai hukumar yansanda ba zata yafe masa ba sai ya fita daga cikin ofishin ya zagaya ta bayan ginin ofishin ya nufi wajen wata rijiya ya tsunduma a ciki lamarin da yayi sanadin mutuwarsa shima.

  Kakakin hukumar yansanda na jihar Ondo Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma kara da cewa rundunar tana shirye shirye akan yadda zata ilmantar da jami'an ta akan yadda zusu kiyaye aukuwar irin wannan lamarin nan gaba yayin da aka adana gawakin mamatan a dakin ajiye gawa a babban Asibiti na garin Ore.


  Shafin mu na Facebook
  https://www.facebook.com/isyakuweb
  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
  Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
  Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Safeton 'dansanda ya kashe DCO akan cin hancin N150.000 Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });