Ababe 11 da ya kamata ka sani gameda Amitabh Bachchan

Amitabh Bachchan dattijo ne da ke tafiya daidai da zamani wadda ake kira da dogo mai zamani ,yayin da wasu ke kiransa da dattijo mai daraja biyu (double personality)..kamar yadda ka sani a rayuwar kowane dan adam shi ma Amitabh yayi fama da irin nasa gwaggwarmayar da rayuwa.

Ga kadan daga tarihin Amitabh Bachchan da ISYAKU ya tattaro:

1  An haifi Amitabh a garin Allahabad a gabacin India a 1942.
2  Amitabh ya koma garin Mumbai a 1969 domin neman aiki jarumi a finafinai.
3  A 1971 Amitabh yayi fina finan "Anand,Parwana da Reshma Aur Shera".
4  Amitabh ya auri jaruma Jaya Bhaduri a 1973.
5  Amitabh ya sami mumunar rauni a cikinsa lokacin fim na "Cooliie" a 1982 lamarinda da yasa shi jinya.
6  Amitabh ya dakatar da yin fim ya shiga siyasa na takaitaccen lokaci daga 1984-1987.
7  1996 Amitabh ya bude kamfanin "Amitabh Bachchan Corporation" wadda ya gamu da matsalolin kudi.
8  Amitabh ya fara shirin "Kaun Benaga Crorepati" da "Who wants to be a millionair" a shekarar 2000
9  A shekara ta 2008 Amitabh ya fara rubuce-rubuce (blogging) daga bisani ya shiga shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter da ya kaishi ga mabiya fiye da miliyan 60 kawo yanzu
10  Amitabh ya fito a matsayin wani bayahude Meyer Wolfsheim a fin na "The Great Gatsby" tare da Leonardo DiCaprio a shekarar 2013.
11  A 2017 an sako wasu fina finai da Amitabh Bachchan ya bayyana a cikinsu kamar "Sarkar 3,Begum Jaan,da kuma Ghazi Attack".



Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Godiya ta musamman ga:
Lucy Handley
Bryn Bache
Matt Clinch

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN