• Labaran yau

  Madugun satan mutane Evans bai mutu ba-'Yansanda | isyaku.com

  Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa madugun da ake zargi da satar mutane Chukwuduneme Onwuamadike wanda aka fi sani da Evans bai mutu ba kuma jami'an tsaron kasar suna ci gaba da bincike a kansa.

  Majiyatmu ta shaida mana cewa mai magana da yawun hukumar 'yansanda Jimoh Moshood ya shaida wa 'yan jarida cewa "Mun samu izinin ci gaba da tare Evans har tsawon wata uku daga wata kotu," in ji shi.

  A watan jiya ne Evans ta hannun lauyansa ya shigar da rundunar 'yan sandan kara a gaban wata babbar kotun kasar, inda yake zarginsu da tsare shi ba bisa ka'ida ba.

  An cafke Evans ne a farkon watan Yuni a Legas tare da wasu mutum shida da ake zarginsu da satar mutane.  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Madugun satan mutane Evans bai mutu ba-'Yansanda | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama