• Labaran yau

  Dattawan kabilar Igbo sun yi watsi da fafutukar kafa kasar Biafra | isyaku.com

  Shugabannin yankin kudu maso gabashin Najeriya, sun yi watsi da kiraye-kirayen ballewar yankin domin kafa kasar Biafra, wanda kungiyoyin IPOB da MASSOB ke yi.
  Taron ya samu halartar ilahirin gwamnonin jihohin yankin, da ‘yan majalisu yankin, sai kuma dattawan kabilar Igbo wato Ohaneze, a garin Enugu.

  Dattawan sun ce suna goyon cigaba da zaman Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa, sai dai akwai bukatar a dauki matakin sake fasalta tsarin tafiyar da al’amuran kasar.

  Takardar bayan taron da shugabannin yankin na kudu maso gabashin Najeriya suka sa wa hannu, ta bukaci gwamnatin kasar ta soma aiwatar da matakan da ake bukata don sake fasalta tsarin tafiyar da harkokin gwamnati.

  Zalika sun kuma bukaci da fara aiwatar da kudurorin taron da aka cimma a taron tattauna matsalolin kasa da ya gudana a shekarar 2014.  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Dattawan kabilar Igbo sun yi watsi da fafutukar kafa kasar Biafra | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama