Birnin kebbi: Ana gudanar da shirin bayar da bashi ga Manoma | isyaku.com


A cigaba da aiwatar da shirin gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kebbi wajen jaddada tare da inganta harkar noma a Najeriya,Gwamnatin jihar Kebbi ta sake kaddamar da shirin bayar da bashin manoma wanda ake sa ran zai inganta harkar noman damanan bana.

Shirin bayar da bashin ta hukumar bayar da bashin manoma na jihar Kebbi (Anchor Borrower Scheme) karkashin shugabancin Alh.Haruna Maitandu ta fara gudanar da harkar cika ka'ida da zai kai ga baiwa manoma bashin.

Dubbannin manoma ne sukayi dafifi wajen da ake gunanar da cika takardu a wajen da aka tsara gudanar da shirin a matakai a ofishin harkar aikin gona da ke unguwar Tudun wada a garin Birnin kebbi a yau Litinin.

Wakilin mu ya shaida mana cewa aikin yana tafiya akan tsari.Wani manomi mai suna Alh.Aminu ya shaida wa wa wakilinmu cewa ya gamsu da yadda ake tafiyar da tsarin shirin bayar da bashin.

Wata majiya ta shaida mana cewa ana kyautata zaton cewa kimanin mutum 15,000 ne zasu amfana da bashin a fadin jihar Kebbi a aji na farko a shirin kafin mutum 10,000 suma su amfana da shirin a aji na biyu a bisa tsari tafiyar da shirin.

Shirin dai ya kumshi ma'aikatan gwamnati masu noma,kungiyoyi, da kuma manoma wanda ake tafiyar da shi ta hanyar amfani da BVN saboda tabbatar da sahihanci.

Bisa ga dukkan alama shirin na bana zai sami gagarumin nassara sakamakon shigowar ma'aikata da suke da sha'awar noma da karuwar kungiyoyi da suka shiga aikin noma har da manoman gado da suka bukaci inganta da fadada sana'ar tasu ta noma.

Tsarin amfani da Hakimai a zaman masu sa hannu tsakanin gwamnati da manomi zai sa manoman suyi amfani da kudaden kamar yadda ya kamata wanda hakan zai sa abinci ya bunkasa a cikin kasa da kuma samar da aikin yi wanda daga karshe zai kore talauci a cikin al'umma.


Isyaku Garba daga Birnin kebbiKu biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN