Ababen da ya kamata a duba a siyasar jihar Kebbi

Zabe na kananan hukumomi a jihar Kebbi wanda ya zama zakaran gwajin dafi ga mai yiwuwa yadda masu kula da yadda lamurran siyasan Najeriya ke gani cewa zai iya kasancewa a zaben Gwamna a jihar Kebbi idan Allaha ya kaimu 2017.

Wani mai fashin baki a lamurran siyasan jihar Kebbi yayi tsokaci inda ya bayyana ra'ayinsa yayin da yake ganin cewa an riga an sami tangarda a tafiyar tun tashin fari,amma ba'ason a gaya wa mahukunta gaskiya saboda wadanda ke kewaye da gwamnati basa son a ce sun kasa.

Alh.Abubakar Arab ya yi nuni da ababe guda uku wanda ya kamata a duba da idon basira a jihar Kebbi.

A koda yaushe wasu kan nuna cewa ai komi yana tafiya daidai akan tsari,amma idan ka duba da kyau  a bisa kididdiga na alkalumma na ra'ayin jama'a da dama akwai ababe uku da suka haddasa shakku da zai iya haifar da damuwa ko matsala a fahimtar tafiyar siyasar jihar Kebbi nan gaba

1.  Wadanda aka same su a cikin jam'iyar APC a jihar Kebbi da yawa suna kukan cewa kyautatawar Gwamnati bai isa garesu ba amma sun ci gaba da yin biyayya ga Gwamnati saboda akida.

2.  Wadanda suka shigo jam'iyar a bisa rabin kansu kuma suke bayar da gudunmawa kafin a kafa Gwamnati suna da nasu koke daban amma suma suna tare da Gwamnati sakamakon biyayya.

3.  Wadanda suka canja sheka daga wata jam'iya,kagan dole ne suyi tunanin cewa a basu kulawa na musamman wanda ya samo asali a kan dalilin cewa sun baro tsohuwar jam'iyarsu ne suka koma jam'iya mai mulki saboda akida.

Kagan a nan dole ne a sa sikelin mutunci da gaksiya domin su bayar da sakamakon da zai haifar da adalci.

Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN