kawanyar da Al-Shabab ta yi wa Mogadishu yazo karshe | isyaku.com

Jami’an tsaro sun kawo karshen kawanya ta wanni 10 da ‘yan ta’addar Al-Shabab suka yi wa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.

Wani jam’in dan sanda Ali Adnan ya shaida wa ‘yan jaridu cewa, ‘yan ta’addar Al-Shabab sun kai dauki kan wani gidan sayar da Pizza bayan kai harin kunar bakin wake a otel din Posh da ke kusa da gurin.

Kakakin ma’aikatar harkokin cikin gida ta Somaliya Ahmad Muhammad ya ce, jami’ansu sun kawokarshen kawanyar da Al-shabab ta yi wa birnin Mogadishu na tsawon awanni 10.

Ya kara da cewa, akalla akwai mata 7 da wani dan kasar Siriya 1 da suka jikkata.

Ya kuma ce, an kubutar da ‘yan kasar Kenya 2 da dan kasar Itopiya daya daga hannun ‘yan ta’addar.
Kungiyar ta’adda ta Al-Shabab kuma reshen Alqa’eda da ke Somaliya ta dauki alhakin kai hare-haren.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Daga shafin TRT

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN