• Labaran yau

  Gwamnan jihar Kebbi ya bayar da kyautar kudi ga Malaman Musulunci a Shanga L.Govt | isyaku.com

  A yau Jumu'a ne 30/06/2017 aka baiwa wasu Malamai masu koyarda addinin Musulunci a karamar hukumar Mulkii ta Shanga kudaden da Gwamnan jihar Kebbi ya bayar domin a basu , wa'yannan malamai dai tuni suka Karbi wa'yannan kudaden  dubu goma-goma , a hannun Bello S Fawa Saminaka.

  Malaman wadanda ke cike da murna da farinciki suka dukufa suna yiwa gwamnan jahar Kebbi addu'a ta alkhairi akan wannan kyauta da yayi zuwa garesu.

  Kadan daga cikin Malamanda suka amfana da kudin akwai :Mal. Yahaya Saminaka (Babban Limamin masallain Jumu'ah na garin Saminaka) Mal. Musa Husaini G/masa , Mal. Dauda Muh'd 'yarbashe , Mal.Abubakar Dogo T/giwa ds. Kuma mafi yawan wannan kyautar tafi shafuwar Malamai masu Almajirai ( Wato makarantar Allo).


  Daga Sani Musa Saminaka


  Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Gwamnan jihar Kebbi ya bayar da kyautar kudi ga Malaman Musulunci a Shanga L.Govt | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama