Birnin kebbi: Tattaki don kiraye ga dan Majalisa | isyaku.com

Da yammacin Juma'a wasu Matasa karkashin jagorancin Muhammad Bello suka yi wani tattaki na lumana a cikin gariin Birnin Kebbi inda masu tattakin suke rike da kwalaye da aka yi rubuce-rubuce wanda ke dauke da kalaman da ke kiraye ga wani dan Majalisa

Masu tattakin sun fara tattakin daga Tudunwada suka biyo ta filin Sarki kana suka shiga ta tsohon garin Birnin kebbi da kewayenta daga bisani kuma suka koma gida bayan jawabi daga Muhammad Bello.

Muhammed Bello ya shaida mana cewa "suna wannan tattakin ne saboda dan Majalisan baya mutunta tsofaffi da sauran jama'ar da yake wakilta"

A yayin da muka tuntubi dan Majalisar a wayar salula bai daga wayar ba kuma bai maido sakon sms da muka tura masa ba domin muji daga bakinsa akan wannan korafe korafe na Matasan da ya kai ga tattaki har izuwa wannan likaci da muka wallafa wannan labarin,amma wata majiya ta shaida mana cewa dan Majalisar yana Saudiyya wajen aikin Umra.


Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN