A ba Igbo kasar su ta Biafra: Wasu Matasan Arewa sun roki Osinbajo | isyaku.com

Matasa daga arewacin Najeriya karkashin wata kungiyar matasa 'yan Arewa sun bukaci shugaban kasa da mataimakin sa da suyi wa Allah da Ma'aikinsa a ba Inyamirai wanda aka fi sani da Igbo kasarsu ta Biafra.

Wannan ya biyo bayan sanya hannu da shugabannin kungiyar suka yi wadanda suka hada da  Ambassada Shettima Yerima, Joshua Viashman, Aminu Adam, Abdul-Azeez Suleiman da Nastura Ashir Sharif a wata takarda da suka mika wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a madadin sauran hadaddiyar kungiyoyin Matasan Arewa.

Matasan sun shaida cewa" sun yi imani da kwarewar mataimakin shugaban kasa wajen warware sarkakiyar matsaloli',sun kuma kara da cewa "Igbo sun kirkiro tsana da kiyayya akan 'yan Najeriya shekara biyar bayan Najeriya ta sami 'yanci  daga kasar Britaniya inda a ranar 15 ga watan Janairu 1966 matasan Igbo da ke cikin sojan Najeriya suka kaddamar da mummunar tawaye mai asali da kabilanci sanadin da suka kashe wasu manya'yan Arewa da daruruwan hafsoshin soja 'yan asalin Arewa a juyin mukin soja na farko a tarihin Najeriya"

A cikin wannan tarzoma na soja ne Igbo suka kashe Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello,da Prayi minista Sir.Abubakar Tafawa Balewa wanda bayan sun bindige shi a garin Lagos suka daura gawarsa a mota landuroba na sojoji suka yi ta jan gawar a titunan garin Lagos,da kuma Sir Akintola Primiya na yankin kasar Yarbawa babu Igbo ko daya da suka kashe a wannan tarzoman juyin mulkin.

"Bayan wannan kisa da ya canja alkiblar Najeriya wajen zamantakewa 'yan kabilar Igbo sun ci gaba da kiran sauran 'yan Najeriya da kalamai irin na zagi,cin mutunci,wulakanci raini da sauransu.A bisa wannan dalili babu yadda za ka iya zama da mutumin da iya abinda ka iya sani game da shi a bisa la'akari da tarihi shine tarzoma,cuta da fitina,Idan basu kasarsu ta Inyamurai zalla Biafra shine zai kawo zaman lafiya a Najeriya ai sai a basu kasar tasu ta Biafra"

Matasan sun nuna yadda kasar Arewa da jama'arta suka karbi Inyamirai ko  Igbo da hannu biyu kuma suka san yadda zaman Arewa yake amma duk da haka basa nuna kauna ga jama'arta,wanda hakan ya haifar da shakku akan amincewa tsakanin Igbo da 'yan Arewa da kuma Yarbawa.@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN