• Labaran yau

  Birnin kebbi: Hauhawan farashin kaji kafin bikin karamar Sallah | isyaku.com

  Shehu Alh.Dan Malam mai kaji mazauni garin Bunza a karamar hukumar mulki ta Bunza a jihar Kebbi mutum ne da ya shafe fiye da shekara 25 yana sana'ar sayar da kaji da zabi wanda yake sayowa daga kauyukan Bunza daga bisani ya shigo da kajin garin Birnin kebbi saboda ya sayar da su.

  Ta la'akari da yadda ake samun hauhawan farashin kayakin masarufi harma da kayan abinci yayin da kaji ma ba'a barsu a baya ba.Dan Malam ya shaida wa ISYAKU.COM cewa a yanzu haka akan iya samun babban zabo a kan N1800 har zuwa N2000,kaji kuma akan samu manya a kan N1500 zuwa 1800 sakamakon karancin kajin da zabi saboda samun karuwar bukatar naman tsuntsayen a yayinda karamar Sallah ke gabatowa.

  Wata majiya tashaida mana cewa akan sami wasu diloli masu sayen kaji da zabin ne da matukar yawa wanda suke tahowa daga makwabciyar mu jamhuriyar Nijar a yinda su masu saye daga Nijar suke biya da Sefa sanadin da ya haifar da babban gibi ta farashi a bisa amfani da Naira wajen biyan kudin kaji da zabbin.

  A kasar Hausa amfani da naman tsuntsaye wani abu ne da ake danganta shi da kasaita ta al'ada musamman a gidajen masu mulki ko hannu da shuni a lokutan shagulgula kamar karama ko babban Sallah,Mauludi bukukuwan aure da sauransu.


  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Birnin kebbi: Hauhawan farashin kaji kafin bikin karamar Sallah | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama